Iran Ta Ce Dole Ne Amurka Ta Janye Mata Takunkuman Tattalin Arziki Masu Gurgurtawa Da Ta Dora Mata

Mataimakin ministan harkokin wajen a kan al-amuran siyasa, dole ne Amurka ta daukewa kasarsa wadannan takunkuman tattalin arziki wanda suke cutar da mutanen kasar Iran

Mataimakin ministan harkokin wajen a kan al-amuran siyasa, dole ne Amurka ta daukewa kasarsa wadannan takunkuman tattalin arziki wanda suke cutar da mutanen kasar Iran da al-adunsa.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto TakhtaRawanchi yana fadar haka a shafinsa na X ko twitter a da, a kuma  jiya Talata, Mataimakin ministan ya kara da cewa, takunkuman tattalin arzikin da kasashen Amurka da Turai suka dorawa kasar Iran ya zuwa yanzu ya shafi rayuwar mutanen kasar da dama wanda kuma take hakkinsu ne.

Labarin ya kara da cewa a shekaru fiye da 40 da suka gabata, gwamnatocin Amurka kadai sundorawa kasar Iran takunkuman tattalin arziki mafi muni, kuma nau’ii daban-daban. Haka ma ta dade tana wa kasar barazanar far mata da yaki, takunkuman tattalin arziki mafi muna, yakin farfaganda na kasya da sauransu.

Duk da cewa gwamnatocin kasar ta Amurka sun kasa cimma manufofinsu na dorawa kasar ta Iran takunkuman tattalin arziki,  Washington ta ci gaba da dorawa kasar wadannan takunkuman tattalin arziki. Duk da cewa hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments