Search
Close this search box.

Iran Ta Ce Aiwatar Da Kisan Gilla Kan Isma’il Haniyeh Dalili Ne Na Keta Dokokin Kasa Da Kasa

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Kisan shahidi Isma’il Haniyeh wani misali ne karara na keta ka’idojin dokokin kasa da kasa Wakilin din din

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Kisan shahidi Isma’il Haniyeh wani misali ne karara na keta ka’idojin dokokin kasa da kasa

Wakilin din din din na Iran a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Geneva ya jaddada cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya ba ta cancanci halaccin da ya wajaba wajen jagorantar wata cibiyoyi na Majalisar Dinkin Duniya ba ciki har da taron kwance damara.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya habarta cewa: Jakadan Jamhuriyar Musulinci ta Iran Ali Bahraini a cikin wata sanarwa da ya fitar a yayin taron majalisar dinkin duniya kan kwance damarar makamai ya bayyana cewa, shugabancin hukuma da ke karkashin Majalisar Dinkin Dujiya yana bukatar kiyaye dokoki da ka’idojin dokokin kasa da kasa da shirye-shiryen hadin kai na duniya.

Bahrain ya kara da cewa: Keta yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da jakadan haramtacciyar haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi a gaban idon duniya a Majalisar Dinkin Duniya na nuni da cewa wannan hukuma ba ta bin ka’idojin Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments