Iran Ta Bukaci Kungiyar BRICS Ta Samar Da Cibiyar Watsa Labarai Ta Kungiyar

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani wanda yake halattan taron ‘Shuwagabannin kafafen watsa labarai da kuma masu Magana a madadin gwanati a ma’aikatun

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani wanda yake halattan taron ‘Shuwagabannin kafafen watsa labarai da kuma masu Magana a madadin gwanati a ma’aikatun harkokin wajen na kasashen kungiyar ta Brics, wanda yake gudana a birnin Mosco na kasar Rasha, ya bukaci kungiyar ta samar da cibiyar watsa labarai ta kasashen kungiyar don kalubalantar cibiyoyin watsa labarai na kasashen yamma. Da kuma karyata labaran boge wadanda cibiyoyin watsa labarai na wadannan kasashe suke yadawa.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Naseer Kan’ani kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya na cewa: Samar da cibiyar watsa labarai na kungiyar zai taimaka mata wajen karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen kungiyar, sannan ya karfafa zumunci tsakanin cibiyoyin watsa labarai na kasashen kungiyar, wadanda zasu fadi labaran gaskiya game da kungiyar, su kuma soke na kariya wadanda suke fitowa daga kasashen yamma.

Ya kara da cewa wannan har’ila yau zai kauda mamayar da kafafen yada labarai na kasashen yamma suka yi a duniya. Sannan hakan zai bayyana fuska biyu wanda kasashen yamma suke nunawa a al-amuran da suka shafi kare hakkin bil’adama da kuma farfagandar karya da suke yadawa a duniya dangane da hakan. Daga karshe Kan;ani ya ce:  samar da irin wannan cibiyar zai samar da wata kafa wacce labaran gaskiya wadanda kuma suke kwatanta adalci za su kwarara zuwa  ko ina a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments