Iran Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Yi Abinda Ya Hau Kansu Na Kare Kasar Yemen Daga Amurka Da Burtaniya

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani yana fadar haka ya kuma kara da cewa

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani yana fadar haka ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Iran tana allawadai da hare haren takala wadanda sojojin kasashen Amurka da Burtania suka kai kan lardunan Hudaida da San’aa na kasar Yemen wanda ya kai ga shahadar wasu daga cikin mutanen kasar.

Ka’ani ya kara da cewa haren da jiragen yakin Amurka suka kaiwa kasar yemen a jiya da dare keta hurumin kasar Yemen kuma take hakkin fafaren hulan da hareharen suka kashe ne.

Tun cikin watan Nuwamban da ya gabata ne gwamnatin kasar Yemen ta shiga yaki don tallafawa falasdinawa wadanda sojojin HKI suke yiwa kaissan kiyashi a gaza, ta hanyar hana dukkan jiragen ruwa masu zuwa HKI.

Ya zuwa yanzu dai hare haren yemen kan jiragen ruwan HKI ko na Amurka da Burtania sun yi tasiri wajen gurgunta tattalin arzikin HKI sannan sun yi tasiri a harkokin kasuwanci tsakanin kasashen duniya.

Daga karshen Naseer Kan’ani ya gabatar da ta’aziyyarsa ga mutanen kasar Yemen da gwamnatin kasar da kuma musamman iyalan gidan shahidan hare haren jiya. Da fatan All..yayi masu rahama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments