Iran Ta Bukaci A Dauke Mata Takunkuman Tattalin Arziki Don Jinya Da Kuma Kare Lafiyar Guragu A Kasar

Gwamnatin kasar Iran ta bukaci a dauke mata takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata saboda ta sami damar shigo da magunguna da bukatun guragu

Gwamnatin kasar Iran ta bukaci a dauke mata takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata saboda ta sami damar shigo da magunguna da bukatun guragu a kasar, wadanda saboda wadannan takunkuman suna hanata tallafawa wadannan guragu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Ali Muhammad Qadri shugaban hukumar jin dadi da walwalan jama’a na JMI yana fadar haka a taron MDD dangane da hakan a birnin NewYork.

Qadri ya kara da cewa takunkuman tattalin arziki kan guragu take hakkin su ne kamar yadda kowa y asana.

A jiya talata ne aka bude taro karo na 17 dangane da kasashen da suka sanya wa kudurin MDD mai suna UN CRPD (COSP17) a birnin NewYork inda kasashen suke tattauna batutuwan da suka shafi guragu da wadanda sukem da tawaye a halittarsu a duniya.

Qadri ya kara da cewa gwamnatin JMI tana tallafawa guragu da wadanda suke da nakasa a halaittansu da al-amura da dama don sawwaka rayuwarsu. Kuma sun hada da samar da dokokin a majalisar dokokin kasar wadanda zasu taimka masu a duk inda suka sami kansu. Shirya tarukan huraswa na guragu, bude masu hanyoyin shiga mutane da hanyar kafafen sadarwa da internet. Amma duk da haka akwai wasu bukatunsu wadanda takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar sun hanasu hakkokinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments