Iran Ta Bayyana Shirinta Na Bude Sabon Shafin Tattaunawa Da Sabuwar Gwamnatin Amurka

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Kasar Iran ta bude kofa don tattaunawa da sabuwar gwamnatin Amurka mai zuwa Mataimakin ministan harkokin

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Kasar Iran ta bude kofa don tattaunawa da sabuwar gwamnatin Amurka mai zuwa

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht Ravanchi ya bayyana cewa: Iran ta bude kofar tattaunawa da sabuwar gwamnatin Amurka mai zuwa, yana mai jaddada cewa duk wani yunkuri na daukan mafi girman matsin lamba kan kasarta ba zai ci nasara.

Majid Takht Ravanchi ya fadi hakan ne a hirarsa da jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya yana mai cewa: Iran ta bude kofar tattaunawa da gwamnatin Donald Trump, amma tana gargadin cewa, duk wani yunƙuri da Amurka za ta yi na sake sanya manufar matsin lamba kan kasarsa da kuma tunanin samun sassauci daga Iran ba zai kai ga nasara ba.

Majid ya kara da cewa: Barazana da tursasawa ba za su yi tasiri ba wajen kawar da takaddamar da ke tsakanin Iran da kasashen Yamma dangane da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.

Takht Ravanchi ya ce: Lokaci ya yi da za a iya hasashen sakamakon yiwuwar huldar da ke tsakanin Iran da Amurka a gwamnatin Trump, ya kuma kara da cewa: Wajibi ne a yi la’akari da manufofin siyasar Amurka dangane da shawarwarinta da kuma sanin yadda za a mayar mata da martani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments