Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa; Ya kamata shugabannin yahudawan sahayoniyya masu nuna wariyar al’umma da aikata muggan laifuka kan bil’Adama da masu goya musu baya daga kasashen yammacin duniya su sani cewa, babu wani abu daga cikin muggan laifukansu da zasu iya rufe gazawarsu a fagen dabarar kalubalantar al’ummar Falastinu masu hakuri da juriya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya jaddada cewa: A cikin kusan watanni goma da yahudawan sahayoniyya suka dauki matakan wuce gona da iri kan Gaza, dalibai kimanin 8,600 da malamai sama da 500 ne suka yi shahada a Zirin na Gaza.
Kan’ani ya kara da cewa; Duk da rufe makarantu da mayar da su matsugunan ‘yan gudun hijira, amma har yanzu wadannan wurare suna ci gaba da fuskantar hare-haren wuce gona da irin sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila bisa dogaro da dalilai na karya marasa tushe, inda a baya-bayan nan suka kai hare-hare kan Makarantar Al-Falah” da ke karkiashin Hukumar kula da harkokin ‘yan gudun hijirar Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya ta “UNRWA”, wadda ke dauke da dubban Falasdinawa ‘yan gudun hijira a yankin Zaytoun, kuma hare-haren suka yi sanadiyar shahadar Falasdinawa masu yawa tare da jikkata wasu na daban.