Iran Ta Bawo Mayakan Huthi Fasahar Kera Makamai Masu Linzami Daga Cikin Ruwa

JMI ta bawa kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen makamai masu linzami wadanda ake iya cillasu daga cikin tekuna mai suna Ghadr. Kamfanin dillancin labaran Tasnim

JMI ta bawa kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen makamai masu linzami wadanda ake iya cillasu daga cikin tekuna mai suna Ghadr.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya ce makamai mai linzami samfurin Ghadir wanda ake iya cilla shi daga cikin teku ya shiga hannun sojojin kasar Yemen sannan bisa bayanan wasu kasashen yamma hakan wani hatsari ne ga kasashen Amurka da kawayenta a yankin, musamman HKI.

Makamin wanda ake iya cillashi daga tekun red sea yana yin barna mai yawa ga makaman makiya.  Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran bata yi wani karin bayani dangane da wannan labarin ba, majiyar ofishin daraktan tsaron kasa na Amurka ta bayyana cewa, JMI tana ta fi ko wace kasa a yankin mallakan makamai masu linzami kuma sune a gaba a duniya wajen kera jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga Nesa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted