Iran: Shigowar HKI Da Barnan Tayi Ne Ya Sa Iran Nemi Kwarewa A Fasahar Nukliya

Shugaban Hukumar makamashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Islami ya bayyana cewa shishigin HKI da kuma barnan da ta yiwa kasar Iran suna daga cikin

Muhammad Islami

Shugaban Hukumar makamashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Islami ya bayyana cewa shishigin HKI da kuma barnan da ta yiwa kasar Iran suna daga cikin abubuwan da suka tilastawa hukumarsa ta bukaci kwarewa a harkokin fasahar Nukliya da kuma tashe makamashin Uranium da kanta, ba tare da dogaro da wata kasa a duniya ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Islami yana fadar haka a wani taro a jiya Laraba a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa. Wannan ne ya tilastawa gwamnatin kasar kafa hukumar makamashin Nukliya mai zaman kanta, duk da cewa samun fasahar yana da matukar sarkakiya, hakama kayakin aikin sarrafa makamashin yuranium duka basa da saukin samu, saboda HKI da kasashen yamma ne suka fi korewa a wannan fannin a lokacinda kuma su suke da kayakin aikin.

Yace, wannan ya tilastawa kasar da farko samarwa, bincike, gwaji, da ginawa, samar da kayakin aikid da kuma fitar da sakamakon da ake bukata. Daga nan ne kasashen yamma musamman Amurka suka kuduri anniyar raba mutanen kasar Iran da wannan fasahar, Amurka ta fada a fili, ko ta lalata wannan fasahar ta hanyar diblomasiyya ko kuma tare da amfani da karfi. Wanda ya zuwa yanzu ta yi amfani da dukkan wadan nan hanyoyi ta kasa kaiwa ga manufarta.

Banda kashe gomomin masana fasahar nukliya na kasar wanda HKI da Amurka suka yi a watan yulin shekara ta 2025 Amurka ta yi amfani da karfin don lalata cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar ta Iran, sai dai duk da cewa sun lalata wani bangare na wadan nan cibiyoyi amma sun kasa hana kasar ci gaba da amfani da wannan fasahar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted