Iran : Pezeshkian, Ya Yi Jawabinsa Na Farko Kai Tsaye Ga Jama’ar kasar

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi jawabi ga al’ummar kasar a jawabinsa na farko kai tsaye ta talabijin, bayan rantsar da shi a matsayin

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi jawabi ga al’ummar kasar a jawabinsa na farko kai tsaye ta talabijin, bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran na tara a wata daya da ya gabata.

A jawabin da ya yi a daren Asabar, shugaban ya sabunta alkawarinsa na yin adalci ga jama’a da yin duk abin da zai iya don magance matsalolin kasar.

Pezeshkian ya kuma yi ishara da alkawarin da ya yi a zaben na samar da fahimtar juna tsakanin ‘yan kasar, inda ya ce tuni ya fara cika wannan alkawari ta hanyar kafa majalisar ministoci da ta kunshi ministocin jam’iyyun siyasa daban-daban.

shugaban ya sake jaddada kiransa ga kungiyoyin siyasa daban-daban na Iran da su ajiye sabanin da ke tsakaninsu a gefe domin yi wa al’umma hidima ta hanya mafi kyau.

Ya ce ya zuwa yanzu, mun yi iya bakin kokarinmu wajen kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Dangane da batutuwan da suka shafi harkokin ketare kuwa, shugaban na Iran ya bayyana cewa: “Muna fuskantar tsauraran takunkumai inda Ya jaddada cewa, Amurka, Turai, da kuma kasashen da ‘yan korensu sun sanya wa Iran takunkumi, kuma ba sa gudanar da harkokin kasuwanci da mu, wanda hakan ya kawo cikas ga huldar tattalin arzikin da aka saba.

Duk da haka, kyautata wa mutane da magance matsalolinsu ba shi da alaka da takunkumi, inji shugaba Pezeshkian inda ya ce ana bukatar zuba jari daga kasashen waje domin samun bunkasuwar tattalin arzikin da kashi 8 cikin 100, Ya kuma ce gwamnatinsa na kokarin inganta daidaito a bangaren ilimi da lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments