Iran: Maikiya Sun Tsara Matakai 7 Na Kifar Da JMI A Rikici Na Farkon Shekara

Shugaban bangaren leken asiri na rundunar kare juyin juya halin musulunci Burgedia Janar Majid Khademi ya bayyana cewa makiya JMI sun tsara matakai har guda

Shugaban bangaren leken asiri na rundunar kare juyin juya halin musulunci Burgedia Janar Majid Khademi ya bayyana cewa makiya JMI sun tsara matakai har guda 7 a rikicin yan ta’adda ta Daesh a farkon wannan shekara a kasar, kuma manufarsu ta karshe ita ce tumbuke gwamnatin JMI.

Khademi ya bayyana haka ne a jiya Laraba a hirar da yayi da kafafen yada labarai a kasar. Ya kuma kara da cewa, Amurka da HKI duk sun tsare kan cewa da farko zasu fara tada zanga-zanga a cikin gida, sannan su a hankali su fara kawo hare-hare, kamar yadda suka yi a cikin yakin kwanaki 12 a cikin watan Yulin shekara ta 2025.

Yace sun bukaci yan ta’adda da magoya bayansu su kai hare hare kan sansanin sojojin kasar da barikokin sojojin kasar da sauran jami’an tsaro don su raunanasu, sannan su kuma zasu shigo da yaki ta sama da kasa don daga karshe ganin bayan JMI.

Sannan sun yi kokarin yada karya kan  yawan mutanen da aka kashe a rikicin su dorawa JMI alhakin kashesu su kuma halattawa kansu shigowa da yaki kan kasar Iran tare da sunan kubutar da mutanen kasar daga gwamnatin JMI ta Iran.

Yace gwamnatocin makiya sun kai hare-hare ta yanar gizo don lalata sadarwa da kuma ayyukan khidimomin mutane a kasar amma duk wannan bai kaisu ga nasara ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted