Mai Yuwa Taron Tehran Ta Zama Masomin Dawo da Tsaro

Kakakin ma’akatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya bayyana cewa, mai yuwa taron kasashe 4 a yau a nan Tehran ya zama harsashen kafa

Kakakin ma’akatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya bayyana cewa, mai yuwa taron kasashe 4 a yau a nan Tehran ya zama harsashen kafa sabuwar kawancen tsaro a yankin yammacin Asia.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Esma’il baghaei yana fadar haka bayan an kammala taron tsaron yankin wanda ya hada kasashe guda 4 Pakistan, Turkiya saudia da kuma Iran a matsayin mai masaukin baki.

Yace, da farko babban hafsan sojojin kasar Pakistan Asim Munir ne ya gabatar da shawarar a ziyarar da ya kawo nan Tehran a makon da ya gabata, bayan da JMI ta amince da haka.

A lokacinda yake amsa tambayar yan jaridu dangane da manufar taron Baghaei ya bayyana cewa, zuwan manya manyan Jami’an tsaro kasashen 3 a nan Tehran don tattauna matsalolin tsaron yankin ne gaba daya, tun bayan yakin da HKI da Amurka suka farwa kasar Iran da yaki a farkon wannan shekarar.  

“From our perspective, the fact that regional countries are seeking to establish, or at least consider, regional security mechanisms based on their own interests and concerns is a welcome development,” he said.

Baghaei ya kara da cewa, a ganinsa, taron manya manyan kasashen yankin dangane da tsaro, ba kuma tare da shigar wata kasa wajen yankin ba, wani ci gaba ne mai muhimmanci sosai. Ya Kafinhaka gwamnatin JMI ta sha bayyana ra’yinta na cewa babu wanda zai samar da tsaro a wannan yankin sai shiri na kasashen yankin su kadai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted