Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fidda bayani kan cewa daga yau Asabar 18 ga watan Octoban shekara ta 2025, kudurin kwamitin tsaro na MDD wanda aka samar don goyon bayan aiwatar da yarjeniyar Nukliyar kasar Iran wacce aka fi sani da JCPOA ya kawo karshe.
Don haka daga yau shirin Nukliyar kasar Iran ta koma karkashen yarjeniyar NPT, kuma za’a yi mu’amala da shirin kamar sauran kasashen karkashin kula na hukumar IAEA.
Tsahar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na bada wannan sanarwan a safiyar Asabar ta kara da cewa dama kudurin na tsawon shekaru goma ne daga yau ta gama aiki. Daga yau shirin Nukliyar JMI zai ci gab aba tare da wani karin ka’idojin da suke cikin yarjeniyar JCPOA ba.
Bayayin ya kara da cewa, manufar samar da yarjeniya ta musamman a shirin Nukliyar kasar Iran wanda ake kira JCPOA ita ce kauda dukkan tababan da wasu kasashen duniya suke da shi dangane da shirin Nukkliyar kasar ta Iran kama a halin yanzu , bayan shekaru 10 yarjeniyar da kuma kudurin duk sun kawo karshe a yau. Daga haka daga yau babu yarjeniyar JCPOA kuma kudurin ya kawo karshen aikinsa.
Kuma yarjeniyar ta cimma manufar samar da ita, na tabbatar da cewa shirin Nukliyar kasar Iran na zaman lafiya ne, babu wani shirin aikin soje a cikinsa. Kamar yadda Hukumar IAEA ta tabbatar. Har’ila yau tare da wannan sanarwan da kasashen turai 3 suka bayar na sake dawo da takunkuman tattalin arziki na MDD kan kasar Iran ya tashi daga aiki tare da karshen kudurin da kuma Yarjeniyar JCPOA.