Rahotanni sun bayyana cewa iran ta yi tir da sanarwar da shugaban Amurka ta fitar na rufe sararin samaniyar kasar venuzuwela kuma ta bayyana shi a matsayin keta dokokin kasa da kasa, da kuma dokokin kula da zirga –zirgar jiragen sama.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Isma’ila Baghae ne ya fitar da wannan sanarwa inda ya jaddada cewa abin da Washington ta kira a matsayin sanarwa wani bangare ne na adawa na dogon lokaci da kokarin karbe ikon kasar venuzuwela, kuma ya bayyana matakin a matsayin na son rai da ya sabama doka.
Wannan sanarwar ta trump ta ja hankali sosai a bangaren diplomasiya da kuma masana harkokin zirga zirgar jiragen sama, inda wasu kwararru ke ganin babu wata kasa da take da ikon rufe sararin samaniyar wata kasa bisa dokokin sufurin jiragen sama.
A baya bayan nan ne shugaban Amurka Donald Trump ya rubuta a shafinsa na sadarwa na truth social na yin barazana a hukumance cewa matuka jiragen sama da da sauran kamfanonin jiragen sama su dauka sararin samaniyar kasar venuzuwela an rufe shi baki daya.
Ana ta bangaren kasar venuzuwela ta yi watsi da wannan sanarwar tare da bayyana ta a matsayin siyasa kuma tana son mayar da kasar saniyar ware maimakon tabbatar da tsaro