Iran: Kakakin majalisar dokoki ya jaddada aniyarsu ta mara wa  zababben shugaban kasa

Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya gana da zababben shugaban kasar, Masoud Pezeshkian, domin taya shi murnar lashe zaben shugaban kasa karo na

Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya gana da zababben shugaban kasar, Masoud Pezeshkian, domin taya shi murnar lashe zaben shugaban kasa karo na 14.

Ganawar ta gudana ne a ofishin Pezeshkian a birnin Tehran,  inda Qalibaf ya jaddada cewa majalisar dokokin Iran za ta ba da cikakken goyon baya ga sabuwar gwamnati.

A yayin taron, Qalibaf ya kuma jaddada cewa, sa ido mai inganci kan ayyukan sabuwar gwamnati domin tabbatar da ci gaban kasa da jin dadin jama’a na daga cikin muhimman ayyukan majalisar dokokin Iran.

A nasa bangaren, Pezeshkian, ya yaba da rawar da mutane suka taka a zaben shugaban kasa karo na 14, yana mai jaddada bukatar hadin kai na gaskiya a tsakanin dukkan sassan jihohi da nufin magance matsalolin mutane da kuma samar da ci gaban kasar.

Pezeshkian ya samu kuri’u sama da miliyan 16 cikin sama da kuri’u miliyan 30 da aka kada a zaben fidda gwani na shugaban kasa, wanda aka gudanar ranar Juma’a.

Fafatawar ta biyo bayan zabe  zagaye na farko ne wanda ya gudana  a ranar 28 ga watan Yuni, duk kuwa da cewa dai babu wanda ya yi nasarar samun lashe zaben a zagaye na farko.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments