Iran: Jagora ya jagoranci zaman makokin shahadar shugaba Raisi da tawagarsa

 A safiyar yau ne Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gudanar da taron tunawa da shugaban kasa da tawagarsa a Husainiyar Imam Khumaini. Kamfanin dillancin

 A safiyar yau ne Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gudanar da taron tunawa da shugaban kasa da tawagarsa a Husainiyar Imam Khumaini.

Kamfanin dillancin labaran iRNA  ya habarta cewa, taron  tunawa da shahadar Sayyid Ibrahim Raisi; Marigayi shugaban kasa, da Hojjat al-Islam Al-Hashem; Marigayi limamin juma’a na Tabriz, Dr. Hossein Amirabdollahian; Marigayi ministan harkokin wajen kasar, Dr. Malik Rahmati; Marigayi gwamnan gabashin Azarbaijan, Janar  Seyed Mehdi Mousavi; shugaban Tawagar ba da kariya ta shugaban kasa da  ma’aikatan jirgin, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei Jagoran juyin juya halin Musulunci a safiyar yau Asabar 25 ga watan Yuni a Husainiyar Imam Husaini (RA) ya jagoranci zaman makokin  tare da halartar shugabannin bangarorin tsaro na soji da sauransu, jami’an gwamnati, baki na kasashen waje, jiga-jigan siyasa, da sauran bangarori daban-daban na jama’a.

An fara taron ne da karatun ayoyi na kur’ani mai tsarki daga bakin Mohammad Hossein Saidian, makarancin kasa da kasa na kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments