Telebijin din gwamnatin Iran ya bayar da rahioton cewa, hukumomin sojin kasar sun ce za a iya ƙara nisan zangon da makamin Khorramshahr zai iya ci, wanda a halin yanzu yana cin nisan zango 2000 ne kawai.
Rahoton ya bayyana cewa wannan sauyi a nauyin makamin zai ba da damar amfani da shi don kai hari kan sansanonin Amurka a Turai.
A wannan gabar, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa shiri da ƙarfafa ikon ƙasa su ne manyan abubuwan da ke hana barazanar waje.
Araqchi ya bayyana cewa dole ne Iran ta kai wani matsayi a fagen soja inda maƙiya za su rasa begen cimma burinsu.
A wata hira ta musamman da Al-Mayadeen, Janar Mohsen Rezaei, Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, ya yi alƙawarin cewa “duk wani sabon hari na Amurka zai fuskanci hare-hare da ke kai hari kan sansanonin sojojin Amurka masu nisa.”