Iran: Imam Sayyid Aliyul Khamnae Ya Ce Ayyukan Hajji Na Tada Hankalin Makiya Musulmi A Dinuya

Jagoran juyin juya halin Musulunci Imam Sayyid  Aliyul Khaminae ya bayyana cewa ayyukan hajji, da taron musulmi a wurare masu tsarki a kasar Hijas yana

Jagoran juyin juya halin Musulunci Imam Sayyid  Aliyul Khaminae ya bayyana cewa ayyukan hajji, da taron musulmi a wurare masu tsarki a kasar Hijas yana tada hankalin makiya a duniya.

Jagoran ya bayyana haka ne a sakonsa ga musulmi, musamman mahajjan bane, wanda za’a karanta cikekken  sakon a madadinsa a filin Arafa a gobe Asabar.

Kamfanin dillancin labaran Iran Press ko {IP} ya nakalto shafin yanar gizo na jagoran ko internet yana fadar haka.  Jagoran ya kuma kara da cewa: Idan mutum ya ga wannan gagarumin taron musulmi, da kuma irin ayyukan ibadun da suke yi, wannan zai sa fahinci cewa musulmi nan gaba zasu sake dawo da matsayinsu a duniya wanda suka rasa tun da dadewa, amma a wani bangaren koma taron da kuma ayyukan ibadun da musulmi suke yi a Hajji yana tada hankalin makiya.

Sakon jagoran ya kara da cewa, al-amarin ‘Bara’a ga Mushrikai, wanda ya zo cikin Alkur’ani mai girma dangane da aikin Hajji, Jagoran yace a bana wannan bara’ar,ko  kuma nuna barranta daga musharikai dole ne ya zarce daga aikin hajji zuwa dukkan kasashen duniya. Dole sauran musulmi a ko ina suke a duniya sakon bara’a daga Mushrikai ya isa garesu.

Ya kuma kara da cewa: Yan’uma maza da mata ku dawo da hankalinku da kuma ayyukanku kusa da gaskiyar hasken da ke cikin ayyukan hajji, sannan ya zamanto kun yi guzurinsa ga yan’uwan maza da maza a kasashenku.

A gobe Asabar ne ake saran wakilin jagoran zai karanta cikekken wannan sakon ga mahajja a filin arafa da ke kudancin birnin Makka mai tsarki.

Aikin Hajji dai wajibi sau daya ga musulmi wanda yake da ikon zuwa, kuma yana daga cikin ginshikan addinin musulunci sannan ana gudanarda ayyukan Hajjin ne a cikin kwanaki 5 a birnin makka da gewayensa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments