Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Taimakon Amurka ga haramtacciyar kasar Isra’ila ya sanya ta zama ja’ira maras kunya, kuma martanin Iran kanta zai kasance daidai da dokokin kasa da kasa
Jakadan kasar Iran kuma wakilinta na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani a yayin taron kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar a yammacin jiya Litinin a birnin New York na kasar Amurka ya jaddada cewa: Iran tana riko da hakkinta na mayar da martani kan harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasarta a lokacin da ya dace. Kuma martanin Iran zai kasance bisa doka kuma karkashin dokokin kasa da kasa, ya kuma jaddada cewa; Amurka da take taimaka wa yahudawan sahayoniyya wajen aikata laifuffuka ta kasance abokiyar tarayyarsu a duk ayyukansu na wuce gona da iri na rashin kunya da tsageranci.
Irawani ya kara da cewa: Dakarun tsaron sararin samaniyar kasar Iran sun kalubalancin makamai masu linzamin haramtacciyar kasar Isra’ila cikin gaggawa tare da dakile mafi yawan makaman tare da dakile barnar da suke son yi, sai dai hare-haren wuce gona da irin sun yi sanadiyyar shahadar jami’an sojan kasar ta Iran 4 da farar hula guda daya, kuma a lokacin kalubalantar wuce gona da irin Isra’ila, ‘yan ta’addan Iran na kungiyar “Rundunar Adalci” da suke samun goyon baya daga kasashen waje a lardin Sistan da Baluchestan sun kaddamar da hari kan jami’an tsaron Iran, inda suka yi sanadiyyar shahadan jami’an tsaro 10.