Iran: Dakarun (IRGC) Sun Kama Wani Jigon Cikin Yan Ta’adda Na Kungiyar  Jaishul-Adal A Gabacin Kasar

Dakarun IRGC na kasar Iran sun kama wani jigo a cikin mayakan kungiyar yan ta’adda ta Jashulm-Adal wanda yake da cibiya a cikin kasar Pakistan.

Dakarun IRGC na kasar Iran sun kama wani jigo a cikin mayakan kungiyar yan ta’adda ta Jashulm-Adal wanda yake da cibiya a cikin kasar Pakistan.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar ta IRGC na cewa sun kama dan ta’addan ne a garin Pishin na gundumar Rask dake cikin lardin sistan Baluchistan da ke kan iyaka da kasar Pakistan a jiya Asabar.

Labarin ya kara da cewa IRGC sun sami nasara kama shi ne bayan ayuka na leken asiri masu yawa da aka gudanar. Bayan da dan ta’addan ya ya tabbatar ya shiga hannu, ya yi kokarinn halaka kansa, amma ya jiwa kansa ciwo ne kawai. Kuma a halin yanzu yana jinya a wani asbiti kafin a kasha gaban kuliya.

Kafin haka dai wannan dan ta’addan ya sha kai hare haren ta’addanci a kan jami’an tsaron kasar Iran a garin Pishin inda, da shi da abokan tafiyarsa suka kai wasu da dama ga shahada a yaynda wasu suka ji rauni.

A cikin watan Decemban shekarar da ta gabata ne, yan ta’adan sun kashe yansanda Iran 11 a ofishinsu dake Pishin sannan wasu da dama suka ji rauni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments