Kasashen Iran da kuma Tajikistan sun cimma kumshin yarjejeniyoyi 13 na hadin guiwa ta fuskar tattalin arziki.
An cimma hakan ne a yayin ganawar da aka yi a ranar Laraba tsakanin masu fafutukar tattalin arziki daga Iran da Tajikistan din.
An gudanar da taron ne a Dushanbe, babban birnin kasar Tajikistan, tare da halartar ministan al’adu, yawon shakatawa da sana’o’in hannu na Iran, da kuma jami’an Tajik.
A wannan karon, shugaban cibiyar kasuwanci da masana’antu ta kasar Iran Samad Hassan Zadeh, ya jaddada muhimmancin raya dangantakar tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu, yana mai nuni da cewa, domin samun saukin kasancewar masu zuba jari na Iran a kasar Tajikistan, ya zama wajibi a warware wasu daga cikinsu.
Samad HassanZadeh ya kuma yi tsokaci kan sana’o’in hannu na Iran, musamman ma kafet, wadanda za su iya taka muhimmiyar rawa a dangantakar kasashen biyu.