Iran Da Sudan Sun Amince Sun Gaggauta Bude Ofisohsin Jakadanci A Tsakaninsu

Ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta sanar da cewa kasashen Iran da Sudan sun amince su gaggauta bude ofisoshin jakadanci a tsakaninsu. An cimma matsayar ne

Ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta sanar da cewa kasashen Iran da Sudan sun amince su gaggauta bude ofisoshin jakadanci a tsakaninsu.

An cimma matsayar ne a ranar 25 ga watan nan a yayin wata ganawa tsakanin ministan harkokin wajen Iran na riko Ali Bagheri Kani, da kuma na Sudan Hossien Ayyaz a cewar tashar talabijin ta Al’Arabiya.

Manyan Jami’an biyu sun tattauna kan yadda za a fadada huldar dake tsakanin Tehran da Khartoum, inda suka amince da gaggauta bude ofisoshin jakadancin kasashensu.

Babban jami’in diflomasiyyar Sudan na daga cikin baki daga kasashen waje da suka halarci jana’izar marigayi shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi da mukarabansa ciki har da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amirabdollahian.

A farkon watan Oktoban shekarar 2023 ne kasashen biyu suka sanar da dawo da huldar diflomasiyyarsu, bayan shafe shekaru bakwai ba huldar jakadanci.

Khartoum ta yanke alakar ne bayan da Saudiyya ta yanke hulda da Jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan zanga-zangar adawa da hukuncin kisa da aka yanke wa Sheikh Nimr al-Nimr a Iran.

Tehran da Riyadh sun maido da huldar diflomasiya shekara guda da ta gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments