Iran Da Siriya Sun Ce Bullar ‘Yan Ta’adda A Kasar Siriya Makircin Amurka Da Na ‘Yan Sahayoniyya Ne

Ministan harkokin wajen kasar Iran da shugaban kasar Siriya sun bayyana abin da ke faruwa a Siriya a matsayin wani bangare na makirce-makircen Amurka da

Ministan harkokin wajen kasar Iran da shugaban kasar Siriya sun bayyana abin da ke faruwa a Siriya a matsayin wani bangare na makirce-makircen Amurka da ‘yan sahayoniyya a yankin

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araqchi a ganawarsa da shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad a birnin Damascus a jiya Lahadi sun tabbatar da cewa: Abubuwan da suke faruwa a kasar Siriya wani bangare ne na makirce-makircen da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kitsa a kan kasar dama yankin baki daya.

Araqchi ya jaddada matsayin kasar Iran wajen goyon bayan gwamnatin kasar Siriya, yana mai cewa kasar Siriya ta fuskanci matsaloli mafi tsanani a baya, kuma tana iya samun nasara.

Araqchi ya yi la’akari da yunkurin kungiyoyin ‘yan ta’adda na baya-bayan nan a matsayin wani bangare na makirce-makircen makiyan yankin, yana mai jaddada cimma daidaiton munanan manufofi tsakanin ‘yan ta’adda da Amurka da kuma ‘yan sahayoniyya na ci gaba da rura wutar rikici da tashe-tashen hankula a kasashen musulmi, da kuma janyo karin tabarbarewar tsaro a yankin.

A nasa bangaren, shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya jaddada cewa: Siriya da sojojinta da al’ummar kasar suna ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda.

Shugaban kasar Siriya ya yaba da irin matsayin da kasar Iran take da shi wajen tallafawa matakan tsaro da zaman lafiyar yankin musamman kasar Siriya inda ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin dukkanin kasashen yankin domin kawar da ta’addanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments