Iran Da Pakisatan Sun Amince Da Farfado da Layin Dogo Tsakanin Istambul, Tehran Zuwa Islamabad

Kasashen Iran da Pakisatan sun amince sun dawo da zirga-zirgan jiragen kasa tsakanin birnin Istambul na kasar Turkiyya zuwa birnin Tehran na kasar Iran da

Kasashen Iran da Pakisatan sun amince sun dawo da zirga-zirgan jiragen kasa tsakanin birnin Istambul na kasar Turkiyya zuwa birnin Tehran na kasar Iran da kuma birnin Islamabda na kasar Pakistan a cikin wannan shekarar.

Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran yanakalto jakadan kasar Iran a Islamabad Dr RezaAmiri Moghaddam yana fadar haka a lokacin ganawarsa da ministan zirga-zirgan jiragen kasa na kasar Pakisatan Mohammad Hanid Abbasi a birnin Isla,abad. Ya kuma kara da cewa zasu farfado da layin dogon a cikin wannan shekara ta 2025 sannan karkashin tsarin nan na ITI masu jigilar kaya da kuma na fasinja.

Labarin ya kara da cewa idan hakan ya tabbata, wannan zai farfado da daya daga cikin layukan dogo masu muhimmanci a Asia. Saboda layin dogon zai Hada yammaci da kudancin Asia ta nahiyar Turai.

Idan hakan ya tabbata dai za’a dawo da harkokin kasuwanci tsakanin kasashen yannkin wanda yake da sauke yake kuma bada riba mai yawa ga dukkan kasashen da abin ya shafa. Sannan zai rage takurawar da kasashen yamma sukewa JMI.  Taron Islamabad zai bunkasa tattalin arzikin kasashen yankin zai kuma sauwwaka zirga-zirgan mutane da kayaki tsakanin kasashen. Abbasi ministan zirga-girgan jiragen kasa na kasar Pakistan yace farfado da layin dogo tsakanin Iran da Pakisatan zai raya zirga-zirgan jiragen kasa a cikin kasar Pakisatan gaba daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted