Iran Da Kasashe 11 Sun Yi Allawadai Da Kai Hari kan Cibiyoyin Nukliya

Kasar Iran da kuma wasu kasashe 11 sun fitar da bayanin hadin giuwa a taron Kwamiti na Farko na babban zauren MDD karo na 81,

Kasar Iran da kuma wasu kasashe 11 sun fitar da bayanin hadin giuwa a taron Kwamiti na Farko na babban zauren MDD karo na 81, inda suke kira da a kawo karshen kai hare hare a kan cibiyoyin Nukliya a duniya wadanda suke karkashin kula na hukumar IAEA mai kula da al-amuran nukliya ta duniya.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto kasashen suna wannan bayanin a jiya Jumma’a , kuma sun hada da JMI da kasashen da suke goyon bayanta, wadanda suka hada da – Russia, China, Belarus, Burkina Faso, Cuba, Eritrea, Nicaragua, Niger, Pakistan, Tajikistan, da kuma Zimbabwe.

Sun bukaci a bawa dukkan kasashen duniya damar amfani da fasahar Nukliya ta zaman lafiya, a matsayin hakkin ko wace kasa a duniya yin haka.

Kasashen sun bayyana cewa, kai hare hare kan cibiyoyin Nukliya ta zaman lafiya a matsayin sabawa dokokin kasa da kasa da kuma tsare tsaren MDD da kuma ta hukumar IAEA.

Sun ce ba kamata a kaiwa cibiyar makamashin nukliya a ko ina yake, a duniya, kuma yin shiru kan wannan batun idan ya faru bai dace ba. Don barazana ce kan cibiyoyin nukliya a duniya.

Daga karshe sun bukaci kasashen duniya gaba daya su hadu gaba daya su kuma nuna Rashin amincewarsu ga hakan, su kuma goyi bayan amfani da makamashin nukliya ta zaman lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted