Kasashen Iran da Bangaladesh sun yi kakkausar suka ga cin zarafin da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza, tare da yin kira ga al’ummar musulmi da su dauki matakin gaggawa na dakatar da yakin kisan kare dangi da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take yi wa al’ummar Palasdinu.
A wata tattaunawa ta wayar tarho a jiya Alhamis, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na Bangladesh Md. Touhid Hossain sun yi musayar ra’ayi kan halin da ake ciki a yankin.
Araghchi ya yi Allah wadai da laifukan da Isra’ila take tabkawa, musamman manufofinta na hana Falasdinawa abinci da Ruwan sha. Ya kuma jaddada muhimmancin kiran taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kuma samar da dukkanin hanyoyin da za a bi don dakile kisan kare dangi da kuma tinkarar laifukan haramtacciyar kasar Isra’ila.
Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma yi gargadi game da yunkurin Tel Aviv na mamaye yankin yammacin kogin Jordan, yana mai bayyana hakan a matsayin wani babban shirin yahudawan sahyoniya na kawar da batun Palastinu.
Ya kuma yi kira ga kasashen musulmi da su dauki kwararan matakai na hadin gwiwa domin dakile kisan kiyashin da kuma kai agajin jin kai ga al’ummar Palasdinu.