Iran Da Armenia Suna Fara Atisayen Hadin Giwa Don Karfafa Tsaron   Kan Iyakar Kasashen Biyu

Sojojin kasa na kasashen Iran ta Armenia sun fara atisayen soje na hadin guiwa a tsakaninsu, don kyautata tsaro na kan iyakar kasashen biyu na

Sojojin kasa na kasashen Iran ta Armenia sun fara atisayen soje na hadin guiwa a tsakaninsu, don kyautata tsaro na kan iyakar kasashen biyu na kuma tsawon kwanaki biyu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ne suke jagorantar wannan atisayen. Da nufin hana fasa korin muggan kwayoyi da kuma sulalewar yan ta’adda suka kan iyakokin kasashen biyu.

Burgediya Janar Sayyid Mortaza Mira’in babban hafsan  sojojin kasa na IRGC ya bayyana cewa, wannan atisayennn   yana nuna irin yadda sojojin IRGC suke da shirin kare kasar daggga duk wata barazana. Da kuma abota da kyautata makobtaka da kasashe mmmakobta.

Labarin ya kara da cewa ana gudanar da rawan dajin ne a kan kan iyakar kasashen biyu na nordooz.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments