Iran: Babu Wani Hari Sai Mun Maida Martani

Iran ta ce babu wani harin da sojojin Amurka ko HKI zasu farwa kasar da su wanda bazata maida martani ba. Kamfanin dillancin labaran Tesnem

Iran ta ce babu wani harin da sojojin Amurka ko HKI zasu farwa kasar da su wanda bazata maida martani ba.

Kamfanin dillancin labaran Tesnem na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baqaei yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Iran tana dogaro da abinda makaman da ta samar da su a cikin gida kuma bata dokaru da wani daga waje.

Baghaei ya ce gwamnatin Iran bata kuma dogara kacokam da hanyar diblomasiyya don warware matsalolinta da makiya ba, idan diblomasiyya ta yi aiki, ba laifi zamu amince da ita, amma kuma kasar a shirye take ta yi amfani da karfi idan makiya sun zami hakan. Ya ce Iran zata maida martani kan duk wani hari da aka kawo mata.

Baghaei ya kara da cewa, Iran bata damu da rikicin da ke faruwa a cikin jami’an gwamnatin Amurka na korar wasu da nada wasu ba, ammam abinda yake fada shi ne mutanen Amurka suna cewa, dalilan da suka jawo rikicewar harkar tashin jiragen sama shi ne tsofan kayakin aikinsu ne. don haka muke cewa maimakon Amurka ta fidda kudi don yakar Iran ta maida hankali wajen magance matsalolin cikin gida mana.

A wani bangare janar Ahmad Vahidi babban kwamandan rundunar IRGC ya ce , ko karamin hari ne makiya suka kaiwa Iran yana iya zama masomin yaki mai tsanani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted