Iran: Ba Za Mu Taba Manta Da Rawar Da Ingila Ta Taka Wajen Kafa HKI A Yankin Asia Ta Kudu Ba

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa, mutanen kasashen Asia ta yamma da kuma sauran kasashen duniya ba za su taba

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa, mutanen kasashen Asia ta yamma da kuma sauran kasashen duniya ba za su taba mancewa da rawan da turawan ingila suka taka wajen samar da HKI a tsakiyar kasashen musulmi ba.

Kamfanin dillancin labaran Parstoday ya nakalto Kan’ani yana fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa, turawan ingila sun yi kokari wajen rarraba kan al-ummar musulmi a yankin Asia ta kudu, sun kuma kafa gwamnatin wariya a tsakiyarsu a karshen yakin duniya na biyu, kuma tun lokacin gwamnatin kasar Burtania take goyon bayan gwamnatin wariya ta HKI a kan kasar Falasdinu da aka mamaye.

Ya ce har yanzun turawan ingila suna goyon bayan kissan kiyashin da sojojin HKI take yiwa al-ummar Falasdinu a Gaza, kuma ita ma tana da hannu dumu dumi a kissan kiyashin da sojojin HKI suke yi a Gaza.

Daga karshen kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya mutanen kasar Iran ba zasu manta da yadda sojojin ibgila suka murkushe borin mutanen kudancin kasar Iran kafin yakin duniya na day aba, wanfa shahid Ra’is Ali Delwar ya jagoranta don nuna turjiya da mamayar da sojojin ibgila a lokacin suke mamaye kudancin kasar Iran.

Ranar  02 ga watan Satumba na ko wace shekara rana ce ta nuna turjiya ta kasa don tunawa da shahid Ra’is Ali Delwar a kasar Iran.

An haifi Ali Delvar a shekara 1882 ya kuma yi shahada a hannun turawan ingila yan mulkin mallaka a shekara ta 1915M. a lokacinda yake yakar turawan ingila a kusancin kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments