A Iran, ‘yan takara shida da zasu fafata a zaben shugaban kasar na ranar 28 ga watan Yunin nan na ci gaba da yakin neman zabe.
Zaben dai za’ayi shi ne shekara guda kafin lokacin da ya kamata a gudanar da shi sakamakon rasuwar shugaban kasar Ebrahim Ra’asi da wasu mukarabansa a yayin wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu ranar 19 ga watan Mayu.
Yakin neman zaben ya hada da muhawara da gidajen talabijin da radiyo na kasar inda ‘yan takaran ke amsa tambayoyi game da manufofinsu.
A ranar 11 ga watan nan ne majalisar shura ta kasar ta sanar da ‘yan takara shida da zasu fafata a zaben bayan tantance daga cikin jerin wadanda suka aje takara a zaben.