Iran: An Yanke Hukuncin Kissa Kan Wanda Ya Kai Hari Kan Ofishin Jakadancin Azerbaijan A Nan Tehran

Kakakin ma’aikatar sharia a nan Tehran ya bada sanarwan cewa , alkalai sun yanke hukuncin kasa kan mutumin da ya kai hari kan ofishin jakadancin

Kakakin ma’aikatar sharia a nan Tehran ya bada sanarwan cewa , alkalai sun yanke hukuncin kasa kan mutumin da ya kai hari kan ofishin jakadancin kasar Azerbaijan a nan Tehran a shekarar da ta gabata.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakkin ma’aikatar shari’ar ya na cewa alkalan sun yanke masa hukuncin, rai don-rai, wato duk wanda ya kashe a kasheshi a kan wannan mutumin saboda kissan da yayi.

Ya kuma kara da cewa, hukuncin da aka yankewa wannan mai laifin ya nuna irin yadda JMI take kula da kuma kare ofisoshin jakadancin kasashen waje a nan Iran.

Ya kuma kara da cewa a halin yanzu an amince da hukuncin, kuma an mikawa jami’an gidan yari na yanki  27 a nan Tehran don aiwatar da hukuncin.

Kafin haka dai a ranar 27 na watan Jenerun shekara ta 2023 ne, aka kai hare-hare da bindiga a cikin ofishin jakadancin Arzarbaijan dake nan Tehran, inda yaka kashe Orkhan Asghary mataimakin shugaban jami’an tsaro na ofishin jakadancin sannan ya raunata wasu 2. Bayan haka ne dai ‘yansan Iran suka kama shi suka tsare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments