Iran: Amurka Ta Shiga Tattaunawa Da Ita Ne Bayan Da Fahimci Daukar Matakin Soja Ba Zai Yi Amfani Ba

 Birgadiya Janar Rasul Sanaei-Rad wanda shi ne babban kwamandan sojan kasa na Iran ya bayyana hakan ne a wurin tunawa da zagayowar ranar ‘yanto da

 Birgadiya Janar Rasul Sanaei-Rad wanda shi ne babban kwamandan sojan kasa na Iran ya bayyana hakan ne a wurin tunawa da zagayowar ranar ‘yanto da garin Khurramshahr daga mamaya sojojin Ba’asiyya na Sadam, a lokacin kallafaffen yaki.

Birgediya janar Sanaei -Rad ya kuma yi ishara da ‘yanto da garin na Khurramshar yana mai kara da cewa; yadda al’ummar Iran su ka yi gwagwarmayar ‘yanto da garin Khurramshahr, bayan tsawon shekaru 8 na yaki, ya sa Amurka ta fahimci cewa yaki da Iran yana da tsada da kuma hatsari; kuma da ace sun san za su yi nasara ta hanyar karfin soja da ba su zauna akan teburin tattaunawa ba.

Janar Sanaei ya kuma yi kira ga al’ummar Iran da su yi tsayin daka wajen fuskantar Amurka da wuce gona da irinta, kamar yadda su ka yi a lokacin yakin tsaron kasa mai tsarki wanda ta dauki shekaru takwas ana yi, da kasashen turai su ka goyi bayansa.

Haka nan kuma ya yi kira da a kare cigaban da aka samu a fagen fasahar makamashin Nukiliya.

Birgediya janar Sanaei-Rad ya kuma ce; Kare karamarmu a wannan lokacin da kuma manufofinmu na nan gaba, suna tana tattare da yin gwagwarmaya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments