Iran: Amurka da kawayenta ne ke tsawaita yakin Ukraine ta hanyar aikewa da makamai

Iran ta yi watsi da ikirarin Amurka, Birtaniya da Faransa game da rawar da Tehran ta taka a yakin da Rasha da Ukraine, inda Iran

Iran ta yi watsi da ikirarin Amurka, Birtaniya da Faransa game da rawar da Tehran ta taka a yakin da Rasha da Ukraine, inda Iran din ta jaddada cewa kasashen Amurka da kawayenta na turai ne suke tsawaita yakin Ukraine ta hanyar aike mata da makamai.

Wakilin dindindin na Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Saeid Iravani ne ya bayyana hakan cikin wata wasika da ya aike wa babban sakataren MDD da kuma shugaban kwamitin sulhu a jiya Laraba, bayan da jakadun Amurka, Birtaniya da Faransa suka yi zarge-zarge a kan Tehran dangane da rikicin da ke faruwa tsakanin Rasha da Ukraine.

Ya ce Iran ta yi watsi da duk wasu zarge-zargen da ke nuna hannunta a sayarwa ko fitarwa, ko mika makamanta ta hanyar  da ta saba wa alkawurran da ta yi na kasa da kasa ga Rasha, yana mai cewa dukaknin kalaman zargi ne kawai maras tushe balantana makama.

Yace, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauki wannan zargi a matsayin irin matakai na siyasa da Amurka da sauran kasashen turai suka saba kirkirowa domin domin cimma manufofinsu a kanta ko kuma wasu daga cikin kasashen da suke kawance da ita.

“Abin mamaki ne da munafunci cewa kasashe uku da ke da hannu kai tsaye a rikicin Ukraine da kuma bayar da gudummawa sosai wajen ci gabanta ta hanyar samar da manyan makamai sun yi wannan ikirarin mara tushe a kan Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments