Iran: Amurka Da HKI Sun Fadi A Yakin Gaza, Kuma Dole A Hukuntasu

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani ya bayyana cewa Amurka da HKi sun rika sun yi asara a yakin da suke fafatawa a

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani ya bayyana cewa Amurka da HKi sun rika sun yi asara a yakin da suke fafatawa a Gaza, kuma lokaci na zuwa sanda za’a gurfanar das u a gaban kotu don laifuffukan da suka aikata.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Kan’ani yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Amurka tana da hannu dumu dumu a ta’;asanda HKI take aikatawa a gaza, don tare da makamai da kuma yardarta ce take aikata wadannan ayyuka.

Kan’ani ya ce ya zama wajibi ga kasashen duniya su nemi jinin Falasdinawa wadanda gwamnatin HKI da kuma Amurka suka zubar a Gaza ba tare da wani hakki ba.

Ya kuma kara da cewa wanda ya fi asara a wannan yakin itace gwamnatin Amurka saboda ya rasa yardar yan kasar da dama, daga ciki hard a wadanmda suka fito zanga zanga zuwa fadar white suna bukatar shugaban Biden ya sanyawa yakin gaza jan layi, bayan wadanda ta sanya amma HKI ta tsallakasu.

Masu zanga zangar sun bukaci gwamnatin Amurka ta dakatar da kissan kare dangin da ake yi a Gaza, sannan ta kawo karshen yakin.

A hare harenta na baya bayan nan dai sojojin HKI tare da taimakon gwamnatin Amurka sun kashe falasdinawa fiye da 200 a wata makarantar MDD a garin Nusairat dake tsakiyar zirin Gaza, inda ta halaka wasu daga cikin fursinonin HKI da suke hannun Hamas sannan ta kubutar da 4 cakal da ransu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments