Iram:Yanayin Mashigar Hurmuz Ba Zai Taba Komawa Kafin Yaki Ba

ministan wajen iran yace batun hurmuz ba zai taba komawa kamar yadda yake kafin yakin da amura ta kaddamar ba

Ministan Harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya fayyace cewa babu wani abu da zai koma daidai da kafin Amurka da isara’ila su kaddamar da yaki kan kasar iran ciki har da yanayin gudanar da lammura a mashigar Hurmuz

Ministan yayi wannan bayani ne a lokacin bikin kaddamar da cibiyar adana bayanai da gidan kayan tarihi na jami’in diflomasiya shahid kamal kharrazai wanda aka kashe a wani harin ta’addancin da Amurka ta isra’ila suka kai a farkon wannan shekarar ta 2026

har ila yau ya kara da cewa an fara samun sauyi daga tushe da kuma dabaru a yammcin asiya wanda ba zai taba komawa kamar kafin fara yakin kwanaki 40 ba ko yakin Ramadan, yace mashigar Hurmuz ta dade abude, ba iran ko oman ne suka damu da daukar wasu matakai a mashigar ruwan, dukkan kasashen biyu suna taimakawa ne wajen samar da tsaro da kare jiragen ruwa dake kai kawo a wajen.

Araqchi ya jaddada cewa kula da tsaron yankin ya doru ne kan kasashen yankin da kansu, ba tare da jingina ku neman kasancewar wasu sojojin kasashen waje ba, yace iran da kasashen yanki ya kamta su zana cikin zaman lafiya ba tare da tsoma bakin yan kasashen waje ba, wannan it ace hanyar da za ta iya samar da zaman lafiya da tsaro a fadin yankin

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted