Ministan tsaron kasar Iraki Thabet Al-Abbasi ya bayyana cewa, Washington da Bagadaza sun cimma daidaito kan jadawalin janyewar dakarun hadin gwiwar kasa da kasa daga Iraki a matakai biyu, yana mai nuni da cewa nan da kwanaki za a rattaba hannu kan wata yarjejeniya dangane da hakan.
Al-Abbasi ya bayyana cewa yarjejeniyar ta kunshi kashi na farko daga wannan watan na Satumba har zuwa watan Satumba na shekarar 2025, wanda ya hada da Bagadaza da sansanonin soji na masu ba da shawara, sai kuma janyewar kashi na biyu daga watan Satumban 2025 har zuwa Satumbar 2026 daga Kurdistan.
Al-Abbasi ya shedawa tashar talabijin ta Al-Hadath cewa, sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin ya yi korafin cewa, shekaru biyu ba za su isa a kammala janyewar ba, amma Baghdad ta ki amincewa da bukatar Amurka na tsawaita lokacin har zuwa shekaru uku.
Amurka dai ta jibge sojoji kimanin 2,500 a Iraki da kuma wasu kimanin 900 a Syria, a matsayin wani bangare na kawancen da ta kafa a shekarar 2014 da sunan yakar kungiyar ISIS, wadda ta hada da dakarun Faransa, da Burtaniya, da wasu kasashe.
Baghdad da Washington sun shafe watanni suna tattaunawa game da rage yawan dakarun hadin gwiwa a Iraki sannu a hankali, amma ministan tsaron na Iraki yana sa ran cewa, yarjejeniyar aka cimmawa, za ta bayar da damar fara aiwatar da shirin da kuma kammala shi cikin kankanin lokaci.