Iraki: An Fara Sanar Da Sakamakon Farko Na Babban Zaben Da Aka Gudanar

A yammacin jiya  ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Iraki ta sanar da sakamakon farko na zaben ‘yan majalisar dokokin kasar na shekarar

A yammacin jiya  ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Iraki ta sanar da sakamakon farko na zaben ‘yan majalisar dokokin kasar na shekarar 2025, tare da tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da inganci ta hanyar amfani da na’urorin lantarki.

A taronta na manema labarai, Hukumar ta bayyana cewa yawan masu kada kuri’a ya kai kashi 56.11% bayan samun sakamako daga kashi 99.98% na rumfunan zabe.

Wannan sanarwar ta zo ne sa’o’i 24 bayan kammala babban zaben da aka gudanar a wannan  Talata, da kuma zabe na musamman da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata, domin zaben ‘yan majalisar dokokin Iraki na shekara ta 2025.

Jimillar masu kada kuri’a sun kai 20,063,773, tare da cibiyoyin zabe 8,703 da rumfunan zabe 39,285.

Hukumar ta ci gaba da bayyana cewa adadin masu kada kuri’a ya yi daidai dari bisa dari. Adadin sojoji da jami’an tsaron da suka cancanci kada kuri’a a zabukan na musamman ya kai 1,313,859, wanda aka raba a rumfunan zabe 4,501.

Ga ‘yan gudun hijira (IDPs), masu kada kuri’a 26,538 ne aka yiwa rajista a rumfunan zabe na musamman guda 97.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (IHEC) ta tabbatar da cewa aikinta ba ya nuna son kai ko Rashin sanin makamar aiki, kuma ta ci gaba da kasancewa mai kre hakkokin dukkan ‘yan takara da kuma ‘yan siyasa. Hukumar ta IHEC ta jaddada cewa ba za a iya daukaka kara a sakamakon farko ba kafin fitar sakamakon  karshe ba.

Hukumar ta tabbatar da cewa, za a sanar da sakamakon karshe bayan an warware korafe-korafe da bin kadunsu, inda ta ce an gudanar da zaben a dukkanin jihohin  kasar bisa ka’idojin kasa da kasa, tare da sanya ido sosai na jami’ai a cikin gida da waje.

Dangane da Bagadaza babban birnin kasar kuwa, hukumar ta IHEC ta bayyana cewa, adadin wadanda suka yi rajista ya zarce miliyan hudu, inda yawan masu kada kuri’a ya kai kashi 48.76%.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments