Hukumar kula da harkokin ‘yan gudun hijirar Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce: Falasdinawa 415,000 ne suka rasa matsugunansu, inda suke rayuwa a cikin makarantunta
Hukumar kula da harkokin ‘yan gudun hijirar Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta sanar da cewa: Sama da Falasdinawa 415,000 da ke gudun hijira a halin yanzu suka samu mafaka a gine-ginen makarantunta da ke Gaza, yayin da wasu dubun dubata ke rayuwa a cikin mawuyacin hali a cikin matsugunan ‘yan gudun hijira na wucin gadi.
A bayanin da ta wallafa a shafinta na dandalin X, mai dauke da faifan bidiyo na ‘yan gudun hijiran Falasdinawa, hukumar ta UNRWA ta bayyana irin wahalhalun da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa suke fuskanta a matsugunan da aka kebe musu musamman mata daga cikinsu.
Daya daga cikin mata ‘yan gudun hiiiran mai suna A’ishatu ta bayyana cewa: Wurin da aka tsugunar da su an gina shi ne domin ilimi, ba gidaje ba ne, inda ta bayyana irin wahalar da ta sha tare da karin kalubalen da mata ke fuskanta da kuma ‘yan mata a cikin yaki.