Babban kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ya bayyana wa kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya cewa: Aiwatar da dokokin Isra’ila kan hukumar UNRWA zai zama bala’i
Babban Kwamishinan Hukumar Kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA), Philippe Lazzarini, ya ce: Aiwatar da cikakken dokar Majalisar Dokokin Haramtacciyar kasar Isra’ila ta Knesset kan hukumar UNRWA zai zama masifa, yana mai gargadin cewa: Rage ayyukan hukumar ta “UNRWA” a wajen tsarin siyasa, kuma a daidai lokacin da kwarin gwiwa daga kasashen duniya ya yi kadan, wanda hakan zai kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.
Shafin watsa labaran Falasdinu na “Wafa” ya bayar da rahoton cewa: A jawabin da ya gabatar ga zaman kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya kan halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, gami da batun Falasdinu, a halin yanzu, Lazzarini ya jaddada cewa: Hukumarsa tana da matukar muhimmanci wajen tallafa wa al’ummar da suka shiga halin kaka-ni ka yi da kuma ci gaba da wanzar da yarjejeniyar dakatar da bude wuta, amma duk da haka a cikin kwanaki biyu, ayyukan hukumar ya tsaya cak a yankunan Falasdinawa.
Ya yi gargadin cewa: Makomar miliyoyin Falasdinawa, da tsagaita bude wuta da kuma fatan samun mafita ta siyasa da za ta samar da dawwamammen zaman lafiya da tsaro na cikin hadari.