Ministan Harkokin Wajen kasar Holland ya bayyana cewa: Za su yi iya ƙoƙarinsu don tallafawawajen ganin an kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta
Ministan Harkokin Wajen Kasar Holland Thomas Berendsen ya tabbatar da jajircewar ƙasarsa wajen yin aiki tukuru don kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta, yana mai nuni ga manyan zanga-zangar da aka gudanar a Amsterdam ranar Lahadi, inda dubban ɗaruruwan mutane suka gudanar cikin haɗin kai da jaddada manufar Falasɗinawa.
A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, Berendsen ya bayyana a cikin wani rubutu a shafinsa na Twitter a ranar Litinin cewa: Zanga-zangar da aka yi a Amsterdam ranar Lahadi ta nuna damuwar dubban ‘yan ƙasar Holland game da halin da ake ciki a yankunan Falasɗinawa da manufofin Isra’ila. Ya jaddada fahimtar gwamnati game da wannan jin takaici da rashin taimako a gaban halin da ake ciki a yanzu.
Ministan Harkokin Wajen na Holland ya jaddada cewa: Gwamnatinsu za ta ci gaba da yin aiki tare da abokan hulɗar Turai da na ƙasashen duniya a ƙoƙarin cimma daidaito a Gabas ta Tsakiya da kuma inganta yanayin jin kai a yankin Gaza, wanda a ƙarshe zai kai ga kafa ƙasar Falasɗinu cin gashin kanta, karkashin tsarin dimokuraɗiyya kuma mai dorewa.