HKI Tana Son Shigo Da Yahudawa Daga Kasashen Duniya Kwararru Da Zasu Bunkasa Tattalin Arzikin Kasar

HKI tana son aiwatar da wani shiri don kara yawan yahudawa a kasar, a dai dai lokacinda take fama da karancin yahudawa a kasar. Tashar

HKI tana son aiwatar da wani shiri don kara yawan yahudawa a kasar, a dai dai lokacinda take fama da karancin yahudawa a kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce a baya dai gwamnatin yahudawan suna son kara yawan  yahudawa musamman a yankin yamma da kogin Jordan, ammam har yanzun shirin baya tafiyar kamar yadda take so.

Labarin ya kara da cewa yawan Palasdinawa a cikin kasar Palasdinu da aka mamaye wata barazana ce babba ga gwamnatin kasar.

Banda haka a cikin yakin watanni 15 da ta fafata da Mutanen yankin Gaza, wasu yahudawa sun fice daga kasar kuma da dama daga cikinsu sun sha alwashin ba za su sake dawowa kasarba. Wasu kuma sun kai ga kona passpot dinsu na HKI tare da nufin ba zasu sake dawowa HKI ba har abada.

Har’ila yau wasu masana sun bayyana cewa duk kokarin da gwamnatin HKI za ta yi na gamsar da yahudawa da ga wasu kasashen duniya dawowa HKI da wuya su sami nasara, musamman ganin a halin yanzu ta shiga cikin yaki wanda ba wanda ya san karshensa ba.

Labarin yace kashi 53% na yahudawan da suke zaune a kasar Falasdinu da aka mamaye sun fito ne daga gabas ta tsakiya da kuma arewacin kasar Amurka. Sanna kashi 36% na yahudawan sahyoniya a HKI sun kaurane daga wasu kasashe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments