Search
Close this search box.

HKI Tana Jin Tsoron Kotun Kasa Da Kasa Ta Fidda Sammashin Kama Benyamin Natanyahu

Gwamnatin HKI tana tsaron yiyuwar kotun kasa da kasa dake Lahe, ta fidda sammashin kama firai ministan haramtacciyar kasar da kuma wasu manya manyan jami’an

Gwamnatin HKI tana tsaron yiyuwar kotun kasa da kasa dake Lahe, ta fidda sammashin kama firai ministan haramtacciyar kasar da kuma wasu manya manyan jami’an gwamnatinsa saboda kai kissan kare dangi a yankin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS na JMI ya nakalto tashar talabijin da ‘12”’ ta HKI tana fadar haka, ta kuma kara da cewa, saboda wannan barazanar Natanyanhu ya kira taron gaggawa na majalisar ministocinsa don tattauna wannan batun  a jiya Alhamis.

Kafin haka dai kotun da kasa da kasa bayan sauraron kasar da kasar Afirka ta kudu ta shigar a kan zargin kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza, ta bukaci haramtacciyar kasar ta dauki matakan ganin bata aikata kissan kiyashi a Gaza ba.

Amma al-amarin ya bayyana ga kowa a duniya kan cewa HKI ta aikata, kuma tana ci gaba da aikata kissan kare dangi a Gaza. Inda ya zuwa yanzu ta kashe Falasdinawa fiye da dubu 34, mafi yawansu mata da yara, kuma tana ci gaba da kashewa.

Kafin taron majalisar ministocin dai Natanyahu ya bayyana cewa HKI tana fuskantar barazanar rushewa da kuma macewa daga doron kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments