HKI Ta Tabbatar Da Cewa Ta Kasa Gane Tsarin Ramukan Hamas Karkashin Zirin Gaza Mai Kama Da Sakar Gizo

Gwamnatin HKI Ta Tabbatar da cewa ta kasa gane tsarin hanyouin karkashin kasa wadanda kungiyar Hamas ta gani a zirin gaza, wanda yake kamar sakar

Gwamnatin HKI Ta Tabbatar da cewa ta kasa gane tsarin hanyouin karkashin kasa wadanda kungiyar Hamas ta gani a zirin gaza, wanda yake kamar sakar gizo-gizo. Kungiyar Hamas ta dade tana wadannan ramuka na karkashin kasa ba tare da HKI ta san da su ba, duk tare da cewa tana da ma’aikatan liken asiri masu yawa hatta a cikin Falasdinawan kansu.

A halin yanzu dai rashin sanin tsarin ramukan na karkashin kasa a Gaza, ya sa sojojin yahudawan sun kasa samun nasara a kan mayakan Hamas watanni kimani 10 da fara yaki a yankin.

Mayakan hamas, ko kuma izzuddeen alkassam dai sun gagari sojojin yahudawan a yakin watannan kimani 10 da suke fafatawa da su saboda wadannan ramuka.

Tashata 12 ta HKI ta nakalto wani babban jami’in sojan HKI, wanda bata ambaci sunansa ba yana cewa, ramukan hamasa a Gaza sun bawa mayakan kungiyar damar yakar sojojin HKI, ko kuma yi masu ba zata, saboda ramukan na karkashin kasa da suka gina.

Ya kuma kara da cewa sojojin HKI sun yi kokarin sanin yadda tsarin hanyoyin karkashin kasar suke amma sun kasa yin hakan.

Wani jami’in sojan HKI ya fadawa tashar ta 12 kan cewa Hamas tana amfani da wadannan ramuka wajen kai hare hare kan sojojin HKI a lokaci guda ta kuma jihohi daban daban sannan su bace a karkashin kasa. Daga karshen labarin ya kara da cewa kungiyar tana amfani da ramukan don shigakar da bukatunsu daga waje, ba tare da wani ya sani ba, kuma HKI zata dauki lokaci mai yawa kafin ta wargaza ko ta gano tsarin ramukan.

Ana saran kungiyar ta gina hanyoyin karkashin kasa a zirin gaza wanda ya kai tsawon kilomita 360. Wannan kuma ya sa samun nasar a kansu yana da wuya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments