HKI Ta Kona Falasdinawa Yan Gudun Hijira Da Ransu A Sansaninsu Da Ke Deir-balah

Sojoji HKI sun kai hare hare kan sansanin yan gudun hijira na Falasdinawa dake kusa da Asbitin Deir Balah, wanda yayi sanadiyyar tashin gobara mai

Sojoji HKI sun kai hare hare kan sansanin yan gudun hijira na Falasdinawa dake kusa da Asbitin Deir Balah, wanda yayi sanadiyyar tashin gobara mai yawa wanda ya yi sanadiyyar kona falasdinawa da dama wasu har mutuwa.

Tashar tlabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa hare haren wadanda sojojin yahudawan suka kai a safiyar yau Litinin sun kona Falasdinawa 3 har lahira a yayinda wasu kimani 70 suka ji rauni.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta bayyana cewa akwai yiyuwar yawan wadanda zasu rasa ransu ya karu saboda akwai wadanda suke da munanan raunuka wadanda ana ganin da wuya su rayu a cikin  wannan halin da asbitocin yankin suke fama da rashin kayakin aiki da magunguna.

Sauran Falasdinawa a sansanin yan gudun hijiran sun yi kokarin kashe wutar da duk abinda suka samu, wadanda suka hada da borguna da kuma ruwa. Sojojin yahudawan dai sun bayyana cewa sun kai hare hare a kan sansanin yan gudun hijira na Deir Balah ne don wargaza kayakin yakin soje na masu gwagwarmaya da ke cikin runfunan yan gudun hijirar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments