Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a kudancin Lebanonda makaman (Phosphorus) wadanda aka haramta amfani da su a duniya da safiyar yau Alhamis.
Jiragen yakin na HKI sun harba wadannan makaman ne dai a gefen garin al-khayam dake kudancin Lebanon.
Sai dai kuma kungiyar Hizbullah ta mayar da martani akan ‘yan sahayoniyar ta hanyar harba makamai masu linzami akan sansanin ‘al-mutillah’wanda ya yi sanadin kashe da jikkata sojojin mamaya masu yawa.
A wata sanarwar da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta sanar da kai wani harin akan sansanin sojojin mamaya dake “Zabdin’ tare da lalata makaman yaki da dama acikinsu.
A jiya Laraba ma dai kungiyar ta Hizbullah ta kai wa sansanin leken asirin sojan HKI na “Arab-aramisha’ hare tare da jikkata sojojin mamaya 14,kamar yadda majiyar HKI ta ambata. Hudu daga cikin wadanda su ka jikkatar suna cikin mawuyacin hali.