HKI Ta Kai Hare-Hare Kan Kudancin Kasar Lebanon Duk Tare Da Tsagaita Wuta Da Hizbullah

Sojojin HKI suna ci gaba da sabawa yarjeniyar tsagaita wuta tsakaninta da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon a makon da ya gabata. Tashar talabijin ta

Sojojin HKI suna ci gaba da sabawa yarjeniyar tsagaita wuta tsakaninta da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon a makon da ya gabata.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar Lebanon (NNA) na fadar haka. Ya kuma kara da cewa sojojin yahudawan sun harba makamin atilari a kan garin Naqura dake kan iyakar kasar da kasar Lebanon. NNA ya kara da cewa, wannan ba shi ne karon farko na keta yarjeniyar ba, tun bayan fara aiki da ita a ranar laraban da ta gabata, kuma sun kashe mutane 2 a kudancin Lebanon bayan fara aiki da yarjeniyar.

Labarin ya kara da cewa a ranar Lahadin da ta gabata ce, gwamnatin kasar Faransa wacce take cikin kwamitin kasa da kasa mai kula, da kuma tabbatar da cewa bangarorin biyu sun kiyaye kuma sun dabbaka sharuddan yarjeniyar. Ta kara da cewa  sojojin HKI sun sabawa yarjeniyar har sau 52 tun bayan fara aiki da ita.

Bayan yakin na watanni kimani 14 ne, HKI a dole ta amince da tsagaita wuta da kungiyar Hizbullah bayan da kasa shiga kasar Lebanon ta kasa. Da kuma dimbin asarar da ta yi a yakin.

Yarjeniyar ta kwanaki 60 ne, kuma ana saran kafin ta kare za’a maida ita na din din din.

Kwamitin kula da yarjeniyar karkashin shugabancin  Amurka ya ce ba zai kammala Shirin aikin fara Sanya ido a kan tabbatar da yarjeniyar tana aikace ba, sai zu wa yau litinin ko kuma gobe talata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments