HKI Ta Bukaci A Samar Da Kwararar Falasdinawa Zuwa Wajen Kasarsu Da Aka Mamaye

Ministan harkokin cikin gida na HKI Bezalel Smotrich  ya yi kira ga gwamnatin kasar ta kodaitar ta kuma yi dukkan abinda zata yi don ganin

Ministan harkokin cikin gida na HKI Bezalel Smotrich  ya yi kira ga gwamnatin kasar ta kodaitar ta kuma yi dukkan abinda zata yi don ganin Falasdinawa da kansu su fara kwarara zuwa wajen kasarsu da aka mamaye saboda bawa HKI fadada kasar zuwa dukkan yankunan kasar Falasdinu da suka mamaye, sannan don kuma debe fatan kafa kasar Falasdinu nan gaba.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Smotrich yana fadar haka a ranar Talatan da ta gabata, wa majalisar gudanarwa na ta jam’iyyar Sahyoniyya ta addini a wani wuri kusa da birnin Ramallah.

Har’ila yau  Smotrich ya bukaci gwamnatin HKI ta kawo karshen a hukumance ga yarjeniyar Oslo ta shekara 1990 da falasdinawa wanda yake maganar warware matsalolin da ke tsakaninta da Falasdinawa cikin ruwan sanyi.

Taron na jam’iyyar sahyoniyya masu kishin addini dai shi shirin tabbatar da ikon gwamnatin su kan dukkan kasar Falasdinu nan da shekara ta 2030. Ya bukaci korar Falasdinawa daga kasar Falasdinu daga Gaza da kuma abinda ya kira lardin ‘ Judea and Samaria’ wanda yake nufin yankin yamma da kogin Jordan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted