Gwamnatin HKI ta bada sanarwan cewa, a cikin sa’o’i 48 da suka gabata sojojinta sun wargaza mafi yawan karfin sojojin kasar siriya da makamansu, wanda ya kai kashi 70-80%.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa, a tashoshin jiragen ruwa na Al-Baida da kuma Laziki sojojin yahudawan sun lalala jiragen ruwan yakin kasar ta siriya manya-manya har guda 15 a ranar litinin da ta gabata.
Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun lalata makamai masu linzami, wadanda suke iya zuwa tazarar kilomita 80-190 a wadannan wurare. Tare da lalata wasu nakiyoyi masu yawa.
Labarin ya ce, jiragen yakin HKI sun kai hare-hare ta sama har sau 350, inda suka lalata makamai masu kakkabo makamai masu linza daban–daban masu yawa. Banda haka jiragen yakin sun kai hare-hare kan wasu masu muhimmanci a kasar a kuma biranen Damascus, Lazikiyya, Homs da kuma Tadmur.
Jaridar ‘ma’arif’ ta HKI ta bayyna cewa sojojin HKI sun kai hare hare kan cibiyoyin tsaro har guda 400 a cikin kasar ta siriya a kuma cikin sa’o’ii 48.