Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza

Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila ta kashe wasu falasdinawa guda 5  yankin gaza a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da suka

Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila ta kashe wasu falasdinawa guda 5  yankin gaza a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da suka cimma tsakaninta da kungiyar Hamas a farkon watan oktoba,

A yau juma’a kafar yada labarai ta falasdinu ta bayyana cewa sojojin Isra’ila sun harbe wani bafalasdine a yankin jabaliya dake arewacin yankin Gaza, haka zalika wani bafalasdine mai suna Mahmud suleman al- wadiya sojojin isaraila sun kashe shi a gabashin shuja’iyya dake makwabtaka da gabashin gaza, gari mafi girma a gaza kuma an jikkata wani dan uwansa,

Har ila yau  hamdi al-barim da mohamma salem qadi sun ji mummunan rauni sakamakon harin da sojojin Isra’ila suka kai musu a khan yunus dake yammacin gaza a yan kwanakin nan,

Tun daga lokacin da Isra’ila ta kaddamar da hare-hare a yankin Gaza zuwa yanzu a shekara ta 2023 sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare – hare a yankuna daban – daban inda akalla sun kashe mutane 1062 tare da jikkata wasu dubbai fiye da 20,000 kuma da suka hada da yara kana 1600 an cafkesu ana tsare da su .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted