Hizbullah : Tsare-tsarenmu Na Daram, Zamu Nada Sabon Shugaba Nan Gaba­_ Qassem

Mataimakin babban sakataren kungiyar Hezbollah, Naïm Qassem, ya yi bayani na farko tun bayan shahadar shugaban kungiyar Hassan Nasrallah, a ranar Juma’a a wani harin

Mataimakin babban sakataren kungiyar Hezbollah, Naïm Qassem, ya yi bayani na farko tun bayan shahadar shugaban kungiyar Hassan Nasrallah, a ranar Juma’a a wani harin da Isra’ila ta kai a kudancin Beirut.

Bayan yabo ga Hassan Nasrallah da “dukkan wadanda sukayi shahada a harin na Isra’ila”, Na’im Qassem ya zargi Isra’ila da kai wa “kowa” hari.

Suna yin kisan kiyashi a kan fararen hula, kuma Amurka tana taimakonsu ta hanyar soja da kudi.”

Duk da asarar wasu shugabanni da sadaukarwa, Hizbullah za ta ci gaba da ayyukanta ba wani canji.

 Mun san yakin na iya daukar lokaci mai tsawo, in ji shi.

Za mu fuskanci kowane hali kuma a shirye muke idan Isra’ilawa suna so su kaddamar da farmaki ta kasa.

 Isra’ila ba za ta taba cimma burinta ba, kuma za mu zabi sabon shugaba a lokacin da ya tsawaka inji Mataimakin babban sakataren kungiyar Hezbollah, Naïm Qassem, a jawabinsa na bidiyo.

Za mu yi nasara, kamar yadda muka yi a lokacin arangamar da muka yi da Isra’ila a shekarar 2006,” kamar yadda ya ambata a karshen sakonsa na bidiyo da aka fiyar yau Litini.

Kungiyar ta kuma ce kayayakinta da duk wani tsarinta na nan daram.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments